Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Ministan tsaron Amurka ya dora laifi kan wasu
2020-04-18 20:09:51        cri

A ranar 16 ga wata, agogon wurin, ministan tsaron kasar Amurka Mark Esper ya zargi kasar Sin da yin rufa-rufa a kan yanayin cutar COVID-19 a kasar, kamar dai yadda sauran 'yan siyasar kasar suke yi wajen neman dorawa wasu laifin. Sai dai kasancewarsa ministan tsaron kasar Amurka, furucinsa ya kuma jawo hankalin al'umma a kan halin da sojojin kasar ke ciki.

 

 

An lura da cewa, a daidai ranar da ya yi furucin, rundunar sojin ruwan kasar ta sanar da cewa, yawan sojojin da suka harbu da cutar COVID-19 a babban jirgin ruwa mai saukar jiragen sama na Theodore Roosevelt ya karu har zuwa 655 bisa gwajin da aka yi musu. Kafin wannan, wani dake cikin jirgin ya mutu sakamakon cutar COVID-19. Ban da wannan, an kuma gano bullar cutar a jiragen ruwa irinsu Ronald Reagan da Carl Vinson da kuma Nimitz. Wata taswira da kafofin yada labarai na Amurka suka fitar a kwanan nan dangane da yanayin sojojin kasar na harbuwa da cutar ta yi nuni da cewa, an gano bullar cutar a sansanonin soja sama da 150 da ke fadin jihohi 41 na kasar, kuma cutar ta fi addabar sojojin ruwan kasar.

 

 

Da a baya an dauki matakan da suka dace, da yanzu yanayin bai kai haka ba. Sabo da a ranar 30 ga watan da ya gabata, kyaftin din jirgin Theodore Roosevelt, Brett E. Crozier ya tura wa manyan jami'an rundunar sojan ruwan kasar wata wasika, inda ya bukaci killace sojojin da ke cikin jirgin, tare da yi musu gwajin cutar. Sai dai a maimakon a karbi shawararsa, sai aka zarge shi da kasa tafiyar da ayyukansa tare kuma da sallamarsa daga aiki. Daga bisani, a yayin zantawarsa da CNN, Mr.Mark Esper, ministan tsaron kasar ya bayyana goyon bayansa kan sallamar kyaftin Crozier, kuma a cewarsa, labarin wasikar ba shi da gaskiya.

Lalle, a yayin da Mr. Mark Esper ke iya kokarinsa na kawar da hankalin al'ummar kasar, shin ina aka dosa dangane da hali da sojojin kasar ke ciki? (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China