Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Zambia: Bude birnin Wuhan ya shaida amfanin matakan da Sin ta dauka na yakar cutar COVID-19
2020-04-09 15:45:42        cri

A yayin da ake fuskantar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, jiya Laraba an fara bude hanyoyin fita daga birnin Wuhan da sauran sassan lardin Hubei wadanda cutar ta fi kamari a nan kasar Sin, inda aka maido da zirga-zirga yadda ya kamata a tsakanin lardin Hubei da sauran sassan kasar. Game da haka, magajin garin birnin Lusaka, hedkwatar kasar Zambia Miles Sampa ya bayyana cewa, matakin bude birnin Wuhan ya nuna cewa, matakan da kasar Sin ta dauka na dakile cutar suna da amfani, za kuma su gabatar da managartan fasahohi ga sauran kasashe.

Miles Sampa ya ce, yanzu haka kasarsa na koyon fasahohin kasar Sin, don hana yaduwar cutar a kasar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China