Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Liberia ta kafa dokar ta baci don dakile yaduwar COVID-19
2020-04-09 13:01:32        cri

Shugaban kasar Liberia George Weah a ranar Laraba ya kafa dokar ta baci, da nufin dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

Bisa umarnin gwamnatin kasar wanda zai fara aiki daga karfe 11:59 na yammacin ranar Juma'a, an wajabtawa dukkan 'yan kasar, har ma da baki 'yan kasashen waje dake cikin kasar da su zauna a gida har tsawon kwanaki 21, shugaba Weah ya sanarwa 'yan kasar a jawabinsa ta kafar yada labaran kasar.

Shugaban ya ce, a tsawon wa'adin da za'a shafe karkashin dokar zaman gidan, mutane za su iya fita waje ne kadai domin neman magani ko bukatun da suka zama dole, da suka hada da abinci ko makamashin girki.

Haka zalika, a tsawon wa'adin dokar zaman gidan, dukkan ma'aikatan gwamnatin kasar za su yi aiki ne daga gida, ban da ma'aikatan dake aiki a ma'aikatar kudi ta kasar, da hukumar tattara haraji, da hukumar kula da sufuri ta ruwa, da ma'aikatar harkokin waje, da kuma ma'aikatan babban bankin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China