Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 ya haura miliyan 1 da duba 350
2020-04-09 12:59:54        cri

Rahotanni da ake fitarwa a ko wace rana game da yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID0-19 a duniya na nuna cewa, ya zuwa jiya Laraba da misalin karfe 10 na safe agogon yankin tsakiyar Turai, an samu karuwar mutanen 6,693 da aka tabbatar sun kamu da cutar a wajen kasar Sin, adadin da ya kai 75,893.

A duniya baki daya, an samu karuwar mutane 73,639 da aka tabbatar sun kamu da cutar, adadin da ya kai 1,353,361, kana an samu karuwar mutane 6,695 da cutar ta halaka, adadin da ya karu zuwa 79,235. Daga cikin wannan adadi, mutane 720,219 da aka tabbatar sun kamu da cutar da mutane 57,369 da suka mutu, duk an same su ne a yankin Turai da cutar ta fi tsakani.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China