Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daraktan WHO: A daina siyasantar da annobar COVID-19
2020-04-09 11:12:54        cri

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bukaci a guji siyasantar da batun annobar COVID-19. Ya ce, "Idan muna son yin galaba a yakin da muke, to bai kamata mu bata lokaci wajen nunawa juna yatsa ba."

Ya kara da cewa, "Hadin kai shi ne kadai mafita da zai ba da nasara a yaki da annobar."

Da yake amsa tambayoyin 'yan jaridu game da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tsuke bakin aljihun Amurka ga hukumar ta WHO, Tedros ya ce, sakon da zai isar ga duniya a wannan muhimmin lokaci shi ne, hadin gwiwa da goyon bayan juna sun fi dacewa, a maimakon siyasantar da batun annobar.

A ranar 8 ga watan Afrilu, kungiyar tarayyar Afrika ta sake yin kira ga duniya baki daya na neman hadin kai domin yaki da annobar. Shugaban kungiyar AU, kana shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya bayyana a wannan lokaci cewa, tilas ne kasa da kasa su hada kai domin cimma nasarar kawo karshen annobar. Ya ce, a madadin kungiyar tarayyar Afrika, ya gode tare da nuna goyon baya ga babban daraktan hukumar WHO bisa ga namijin kokarin da yake wajen tafiyar da ayyukan hukumar yayin yaki da cutar ta COVID-19. Cyril Ramaphosa ya ce a wannan lokaci da ake ciki a yanzu, annobar tana ci gaba da bazuwa kuma dukkan kasashen duniya suna fuskantar wahalhalu masu yawa. A wannan lokacin da ake ciki, ya kamata a yi aiki tare domin kawo karshen wahalhalun da ake fuskanta, maimakon a bata muhimmin lokaci wajen gabatar da zarge zarge ga wasu mutane, ko wasu cibiyoyi ko kuma wasu kasashen duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China