Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Son kai na Amurka ya sa ta kwace wasu marufan hanci da baki
2020-04-08 21:30:51        cri

Tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, an sha labarta cewa, Amurka ta mallake wasu marufan hanci da baki, da sauran kayayyakin kariya mallakar wasu kasashe, wadanda wasu daga cikinsu kawayenta ne. An ce kari kan hakan, Amurka ta fara aiki da dokar kera kayayyakin tsaron kasa, don hana sayar da kayayyakin kariyarta ga kasashen ketare, dokar da aka tsara a lokacin yakin Koriya.

Dangane da lamarin, kawayen Amurka da dama sun kiyaye kayayyakinsu ta hanyar musamman, tare da yi suka kan abubuwan da Amurka ta aikata, sun kuma nuna bacin ransu sosai. Ga alama dai ainihin ma'anar tunanin "mayar da Amurka a gaba da komai" shi ne kare moriyar kasar Amurka, ta yadda hakan zai fi tsarin kasa da kasa, da kuma kawayenta muhimmanci.

Hakika dai, abubuwan da Amurka ta yi suna bata huldar da ke tsakaninta da kasashen Turai.

Dangane da yadda Amurkan ta kwace kayayyakin kawayenta ba tare da jin tausayi ba, jaridar Le Monde ta Faransa ta wallafa wani bayani, wanda wani masani mai suna Piotr Smolar ya rubuta a kwanan baya, inda masanin ke cewa, barkewar annobar COVID-19 ta kara gurgunta huldar da ke tsakanin kasashen Turai da Amurka, wadanda da ma akwai sabani a tsakaninsu.

A daya bangaren kuma, jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya ta ce, wannan ne lokaci da kasar Amurka da kasashen Turai suka fi yin nesa da juna a tarihinsu, tun bayan shekarar 1941.

A baya dai, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya bayyana cikin wani jawabinsa cewa, mun yi karya, mun yi magudi, kuma mun saci abubuwa. Yanzu kuwa ya fi kyau ya kara da cewa, mun yi fashi. Duba da abubuwan da Amurka ta aikata, tsohon shugaban kwamitin Turai Donald Tusk, ya ce "idan muna da wata abokiya kamar Amurka, to, ba mu bukatar abokiyar gaba." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China