Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ganin bayan annoba a fadin duniya burin daukacin wadanda suka kwanta dama
2020-04-04 21:22:24        cri
Ranar 4 ga watan Afrilu, rana ce ta bikin share kaburbura na gargajiyar kasar Sin, inda Sinawa kan tuna da wadanda su ka kwanta dama. Domin alhinin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar numfashi ta COVID-19, an yi zaman makoki a fadin kasar, kuma wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta gudanar da makoki bisa doka, bayan aukuwar annobar ba zato ba tsammani, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana girmama moriya da rayukan al'ummun kasar.

Hakika girmama rayuka buri ne na gwamnatin kasar Sin yayin da take kokarin dakile annobar a cikin watanni biyu da suka gabata, har kullum shugaban kasar ya kan jaddada cewa, dole ne a sanya tsaron rayukan al'ummun kasar a gaban komai.

Bruce Aylward babban mashawarcin babban jami'in hukumar lafiya ta duniya ya taba rangadin aiki a kasar Sin, domin nazarin matakan yaki da annobar da kasar ta dauka, daga bisani ya bayyana cewa, ana amfani da daukacin kayayyakin da ake da su domin kandagarkin annobar a kasar Sin, kuma likitocin kasar sun yi kokari matuka wajen ceton rayukan jama'a, kuma abubuwa sun shaida cewa, kasar Sin ta dauki matakan da suka dace, haka kuma ta yi nasarar hana yaduwar annobar.

Amma abun takaici shi ne, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen yamma suna bata sunan kasar Sin domin samun moriyar da suke bukata, har suka yi watsi da kashedin da kasar Sin ta yi da kuma bayanan da ta samar musu a kan lokaci, musamman ma mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, inda sun gaza sauke nauyin dake wuyansu saboda ba su dauki matakan da suka dace ba.

Hakika a ko da yaushe, kasar Sin tana nacewa kan manufar sahihanci ba tare da rufa rufa ba, kuma tana sauke nauyin dake wuyanta, har ta kan hada gwiwa da sauran kasashen duniya, ciki har da Amurka. Kawo yanzu gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar da kayayyakin kandagarkin annobar ga kasashen duniya 120 da kungiyoyin kasa da kasa 4, kana ta tura tawagogin likitoci zuwa kasashe da dama domin taimaka musu. Ban da haka, kasar Sin tana bayyana dabarun yaki da annobar ga kasashen duniya sama da 180 da kungiyoyin kasa da kasa sama da goma domin ceton karin rayuka, bisa la'akari da cewa, kwayar cuta tana shafar daukacin kasashen duniya, kuma bil Adama suna da makoma guda daya, kana taimakawa wasu yana nufin taimakon kai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China