Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin gwamnatin Nijar sun harbe masu tsattsauren ra'ayi 63 har lahira a yankin yammacin kasar
2020-04-04 15:24:41        cri

Ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta sanar da cewa, a ranar 2 ga wata, sojojin gwamnatin kasar sun harbe masu tsattsauren ra'ayi da yawansu ya kai 63 a yankin Tillaberi dake yammacin kasar.

Sanarwar ta bayyana cewa, yayin da sojojin gwamnatin suke gudanar da aikin yaki da ta'addanci a yankin, sun yi musanyar wuta da masu tsattsauren ra'ayin, inda suka kashe 63 daga cikinsu, tare kuma da samum wasu babura da makamai, sai dai sojojin gwamnatin hudu sun rasa rayukansu a fagen dagar.

Yankin Tillaberi na yammancin kasar ta Nijar, na kusa ne da iyakar kasashen Mali da Burkina Faso. Kuma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, masu tsattsauren ra'ayi dake da nasaba da kungiyar IS da sauran kungiyoyin ta'addanci suna ta kai hari yankin, lamarin da ya yi sanadin asarar rayukan mutane da dama.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China