Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yau an yi zaman makoki a duk fadin kasar Sin
2020-04-04 11:45:03        cri

A yau ranar 4 ga wata, an yi zaman makoki a duk fadin kasar Sin da zummar ta'aziyyar jaruman da suka sadaukar da rayukansu, wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da annobar. A lokacin, an saukar da tutoci zuwa rabin sanda a duk fadin kasar Sin, da kuma ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen waje, da tsayar da dukkanin harkokin nishadi a kasar. Kuma daga karfe 10 na safe, al'ummar kasar Sin sun yi shiru na mintuna 3, yayin da motoci, da jiragen kasa, da jiragen ruwa suka rika ham, kana an kunna jiniyar gargadi. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da wasu shugabannin JKS da na gwamnatin kasa sun je dakin Huairen dake Zhongnanhai, inda suka yi shiru na mintuna 3 a matsayin makokin jaruman da suka sadaukatar da rayukansu, wajen yaki da annobar, da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da annobar.

Da safiyar yau, an yi bikin saukar da tuta zuwa rabin sanda a dandalin Tian'anmen dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

"Shahidai" shi ne sunan da kasar Sin ta ba al'ummar da suka sadaukar da rayukansu domin kare kasa da zaman takewar al'umma da ma jama'ar kasa. Wasu daga cikinsu su jami'an lafiya ne da suka yi jinyar wadanda suka kamu da cutar, wasu 'yan sanda ne masu kiyaye tsaro, wasu su masu aikin sa kai ne a cikin unguwanni. Sinawa suna kiransu mutane mafi soyuwa a garesu, kuma al'ummar kasa za su tuna da gaggaruman ayyukan da suka yi.

Annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ta yadu cikin sauri a fadin kasar Sin, ta sa an sha wahalar ayyukan kandagarki, irin wadda ba a taba gani ba tun bayan kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ya zuwa ranar 3 ga wata, gaba daya akwai mutane 3335 da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a Sin. Kuma ya zuwa yanzu, a kalla jami'an lafiya 46 sun sadaukar da rayukansu, wajen yaki da annobar. Kana, cikin watanni biyu da suka gabata, masu aikin ceto a lardin Hubei guda 1500 sun kamu da wannan cuta. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China