Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi zaman makoki da zummar ta'aziyyar jaruman da suka sadaukar da rayukansu
2020-04-04 11:23:19        cri
Yau Asabar, 4 ga watan Afrilu, rana ce ta sharar kaburbura na Qingming ta kasar Sin. Sinawa su kan tuna da kaka da kakanninsu, tare da zaman makokin jaruman kasar, domin tunawa da gagaruman abubuwan da suka yi, da sa kaimi ga al'ummomin kasar da su dukufa don neman ci gaba.

Ya zuwa jiya, 3 ga wata, akwai jimilar mutane 3335 da suka rasa rayukansu sakamakon cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin. A yau, an yi zaman makoki a duk kasar, inda aka saukar da tutoci zuwa rabin sanda a duk fadin kasar Sin da kuma ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen waje, an kuma dakatar da dukkanin harkokin nishadi a kasar. Da karfe 10 na safiya, al'ummar kasar Sin sun yi shiru na mintuna 3, yayin da motoci, da jiragen kasa, da jiragen ruwa suka rika ham, sannan an kunna jiniyar gargadi, a matsayin makokin jaruman da suka sadaukar da rayukansu, wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da annobar.

Bisa kididdigar da aka yi, ya zuwa yanzu, akwai jami'an lafiya akalla 46 da suka sadaukar da rayukansu wajen yaki da annobar. A ranar 8 ga wata kuma, za a bude birnin Wuhan, da aka killace a ranar 23 ga watan Janairun bana. Kana, budewar wannan birnin zai zama babbar alama ta juyayin jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin kare wannan birni.

Ba a kasar Sin kadai ba, akwai jarumai cikin kasa da kasa, wadanda suka sadaukar da rayukansu domin kiyaye al'ummomin kasashensu, da nufin tunkarar wannan annoba dake yaduwa cikin kasa da kasa, wadda ba a taba ganin irinta ba.

A kasar Italiya, likita Marcello Natali mai shekaru 57 ya yi kuka kan karancin safar hannu na likitoci, yayin da yake ceton wadanda suka kamu da cutar a yankin Lombardia, inda aka fi fama da annobar. A karshe dai, ya rasa ransa sakamakon cutar.

A kasar Masar kuma, shehun malami na jami'ar Azhar, kana shugaban sashen nazarin ilmin likitanci Ahmed Al-Louwah, ya mutu sakamakon kamuwa da annobar, kuma ya fidda labarin karshe ta shafinsa na FACEBOOK, domin kira ga al'umma da su zauna a gida na makwanni biyu.

A kasar Rasha kuma, Denis Protsenko, babban likita a asibitin musamman dake jinyar wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Moscow, ya kamu da cutar. A makon da ya gabata ma, ya raka shugaban kasar Vladimir Putin, wanda ya kai ziyara asibitin.

A halin yanzu da ake fuskantar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasa da kasa, a wannan bikin gargajiya na kasar Sin na Qingming, ana zaman makokin jami'an lafiya da suka sadaukar da rayukansu domin yaki da annobar, da kuma nuna girmamawa ga wadanda suke ci gaba da yaki da annobar. Bari mu nuna kaunarmu ga zaman rayuwarmu a nan duniya, da kuma yin fatan alheri ga makomarmu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China