Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har yanzu 'yan siyasar Amurka suna fama da yada jita jita ba tare da la'akari da tabarbarewar yanayin cutar Covid-19 da kasar ke ciki ba
2020-04-03 15:09:18        cri





"A daidai wannan lokaci, a matsayinsu na 'yan siyasa, ya kamata su dora rayukan al'umma da lafiyarsu a gaban harkar siyasa, kuma rashin kunya ne, yadda ake ci gaba cusa siyasa a ciki batun. Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ce ta fadi hakan, a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Alhamis, inda ta bayyana ainihin gaskiyar lamarin, tare da soki 'yan siyasar kan kalamansu na rashin kunya.

Kawo yanzu, yawan mutanen da suka harbu da cutar numfashi ta Covid-19 ya zarce dubu 210, kuma ko a ranar 1 ga wata, akwai mutane sama da 900 da suka mutu a sakamakon cutar. Shugaban kasar ma ya sanar da cewa, kayayyakin kiwon lafiya da aka ajiye na ko ta kwana ma sun kusan karewa. Amma duk da haka, 'yan siyasar kasar suna fama da shafa wa wasu kashin kaji, a maimakon su yi kokarin daukar matakan dakile cutar.

Kwanan baya, da yake amsa tambayar mai gabatar da shiri na kafar CNN, game da me ya sa Amurka ba ta dauki matakai na tinkarar cutar cikin lokaci ba, mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya amsa da cewa, "idan da a baya kasar Sin ta samar da karin alkaluma, lalle halin da muke ciki ba zai kai na yanzu ba." Baya ga haka, sakataren harkokin waje na kasar Mike Pompeo, a yayin da yake zantawa da manema labarai, shi ma ya sake zargin kasar Sin da yayata bayanai, na rashin gaskiya dangane da cutar.

'Yan siyasar Amurka suna bata lokaci, da kuma rayukan al'umma bisa ga yadda suke kare aniyarsu, ta dora laifi a kan wasu, musamman a wannan lokacin da ake cikin a mawuyacin hali na fuskantar cutar COVID-19. 

Amma shin da gaske ne kasar Sin ta boye halin da ake ciki? Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fi iya magana, ba su 'yan siyasa masu karya ba. A gun taron manema labarai da aka shirya a ranar 1 ga wata, Mr. Michael Ryan, jami'in kula da al'amuran gaggawa na hukumar WHO ya karyata zargin da aka yi wa kasar Sin cewa, wai ta yi rufa rufa a kan alkalumanta. Ya kuma yi gargadin cewa, kada a alakanta barkewar cutar a wasu sassan duniya da maganar wai rashin hadin gwiwa, ko kuma yin rufa rufa kan halin da ake ciki.

Wakilin hukumar WHO a kasar Sin Gauden Galea, wanda ya sa hannu a ayyukan dakile cutar a kasar Sin, shi ma ya yi bayani a kan lokacin da kasar Sin ta sanar da yanayin cutar tun farkon fari: wato a ranar 31 ga watan Disamban bara, wato jajibiren ranar rufe kasuwar sai da kifaye da ke birnin Wuhan, inda ofishinsa ya samu kwarya-kwaryar sanarwa daga bangaren Sin.

A ranar 1 ga watan Janairun kuma, an kira taro ta wayar tarho a tsakanin ofishinsa da hedkwatar WHO a birnin Geneva, kuma kafin ranar 3 ga watan, sai da aka kafa tawagar tinkarar cutar a hukunce. Ya zuwa ranar 20 zuwa 21 ga watan Janairun kuma, jami'an ofishin wakilin WHO a kasar Sin sun kai ziyara birnin Wuhan.

 

Mr. Gauden Galea ya kara da cewa, saboda yadda kasar Sin ta sanar da WHO halin da ake ciki a kan lokaci ne, ya sa aka share fagen nazarin cutar, da kuma gargadin sauran kasashen duniya.

To, amma wane mataki ne gwamnatin kasar Amurka ta dauka daga bisani?

Kasancewarsa mai daukar nauyin jagorantar aikin kandagarkin cututtuka na Amurka, ko Mr. Pence zai iya bayyana dalilin da ya sa bayan da likitar kasar Helen Y. Chu ta gargadi kasar kan yanayin annobar a kasar a watan Janairun, kafin daga bisani a watan Faburairu ta sanar da hukumar kasar kan sakamakon gwaji, sai ya umurci a rufe bakinta, da kuma dakatar da gwaje-gwajen? Kana kuma a matsayinsa na babban jami'in diplomasiyya a kasar, ko Mr. Pompeo zai iya bayani kan wadanne matakai ne ya dauka ta fannin hadin gwiwar kasa da kasa wajen shawo kan cutar, da ma kare lafiyar al'ummar kasar tun bayan barkewar cutar? Shin kuma me ya sa cibiyar takaita cututtuka ta CDC ta kasar ta daina samar da alkaluman da suka shafi yawan mutanen da aka yi wa gwaje-gwaje, da kuma yawan mamata tun daga ranar 2 ga watan Maris da ya wuce.

Ko suna iya amsa jerin wadannan tambayoyin? Shin wane ne ke boye yanayin annobar da ake ciki?  

Lamarin kuma ya shaida wani sakon sirri da kafar yada labaran siyasa ta The Daily Beast ta fitar kwanan baya, sakon da ya nuna cewa, fadar White House na shirin hada kan hukumomin kasar da dama, wajen zargin kasar Sin da boye yanayin cutar, da kuma haddasa annobar a fadin duniya, tare da bukatar su jaddada cewa, komai ya faru ne sabo da kasar Sin.

To, in an yi la'akari da abubuwan da suka faru, za a gane cewa, 'yan siyasar Amurka na kokarin aiwatar da shirin, kuma suna kokarin dora laifin annobar kan kasar Sin, don kawar da hankalin al'umma kan yadda suka yi sakaci da aikinsu.

Akwai masu bibbiyar kafofin sada zumunta a Amurka da suka bayyana cewa, "ga Mr. Pence mai fuskar karya", "Gwamnati mai ci yanzu na kokarin dora laifinsu kan wasu, don boye yadda suke yi sakaci da aikinsu."

Yanzu abin gaggawa shi ne a dauki matakai na shawo kan cutar, kamata ya yi 'yan siyasar Amurka su daina yada jita jita, kuma a maimakon haka, su dora rayukan al'umma da lafiyarsu a gaban komai.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China