Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in AU ya yabawa Sin bisa tallafawa yaki da cutar COVID-19
2020-04-03 10:13:00        cri
Mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Kwesi Quartey, ya yabawa matakan da kasar Sin ke dauka da kuma kokarin da take yi wajen yaki da annobar cutar COVID-19, kana da yadda kasar ke ci gaba da tallafawa Afrika a yaki da annobar.

Ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ganawa da jakadan kasar Sin a AU, Liu Yuxi, wanda ya gudana a helkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

A wata sanarwa da Quartey ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce, sun tattauna ne game da yadda za'a kara yin hadin gwiwa da zurfafa cudanya tsakanin kungiyar AU da kasar Sin wajen yakar annobar COVID-19 a Afrika.

Taron bangarorin biyu yana daga cikin kokarin da hukumar gudanarwar AU take yi da nufin dakile annobar ta COVID-19, da nufin zurfafa hadin gwiwa tsakanin AU da kasar Sin don kawar da cutar COVID-19 a Afrika, karkashin dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China