Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AfDB ya samar da dala miliyan 2 don yaki da cutar COVID-19 a Afrika
2020-04-02 11:19:15        cri

Bankin raya cigaban Afrika (AfDB) ya sanar cewa, ya samar da kudade kimanin shillings miliyan 208 na kudin kasar Kenya kwatankwacin dala miliyan 2 domin bada tallafin gaggawa ga hukumar lafiya ta duniya WHO don yaki da cutar COVID-19 a Afrika da kuma rage mummunan tasirin da cutar zata haifar a nahiyar.

Bankin AfDB yace, hukumar WHO a Afrika zata yi amfani da kudaden ne wajen bunkasa shirin yaki da annobar a kasashen Afrika 41, wajen kandagarkin cutar da gwaje gwajen cutar da kuma kulawa da masu harbuwa da cutar.

A sanarwar da bankin ya fitar yace, tallafin zai taimakawa kasashen nahiyar wajen daukar kwararan matakai bayan da aka gano masu dauke da kwayar cutar COVID-19 cikin sa'o'i 48 da kuma taimakawa hukumar WHO a shiyyar Afrika wajen isar da sakonnin wayar da kan al'ummomin yankin.

Sanarwar ta ce, tallafin zai taimakawa shirin ko-ta-kwana na hukumar WHO na dala miliyan 50, wanda hukumomin agaji da suka hada da MDD suke tallafawa shirin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China