Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Donald Trump: za a shiga tashin hankali a cikin makonni biyu masu zuwa a Amurka
2020-04-01 13:28:14        cri

Jiya Talata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a gun taron manema labarai da fadarsa ta gabatar cewa, Amurka na fuskantar kalubale mai tsananin da ba a taba gani a tarihi ba, kuma za a shiga tashin hankali cikin makonni biyu masu zuwa. Kuma ya jaddada cewa, aikin yaki da kandagarkin COVID-19 na shiga wani muhimmin lokaci.

Ma'aikaciyar fadar White House mai kula da aikin yaki da cutar, Deborah Birx ta gabatar da rahoton yakar cutar a gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana. Rahoton ya bayyana cewa, yawan mutanen da ake zaton za su rasa rayuka sakamakon cutar a kasar Amurka zai iya kai dubu 100 zuwa dubu 240, duk da matakan da za a dauka, amma idan ba a dauki matakai ba, adadin zai iya kai tsakanin miliyan 1.5 zuwa miliyan 2.2.

Kafin haka, kwalejin nazarin aikin likitanci na jami'ar Washington ta gabatar da wani rahoton da ya yi hasashen cewa, lokaci mafi tsananin cutar a Amurka zai fara ne a watan Afrilu, sa'an nan zai dade har zuwa watan Yuni. Ban da haka, mai yiwuwa cutar za ta sake bulla a kasar a lokacin kaka ko na sanyi na bana. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China