Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shanghai: An sanya hannu kan ayyukan kwangila 152 na dala biliyan 62
2020-04-01 12:01:59        cri
A jiya Talata ne aka sanya hannu kan wasu ayyukan na samar da sassan na'urorin laturoni da dai sauransu, har 152 a birnin Shanghai na kasar Sin, wadanda darajar su ta kai yuan biliyan 441.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 62.4.

Rahotanni na cewa, ayyukan sun kunshi samar da wasu sassan na'urori da ake amfani da su a injuna, da na'urorin masu kwaikwayon tunanin bil Adama, da na aikin likitanci, da na binciken sararain samaniya, da na samar da hajojin masana'antu, da fannin makamashi da ake sabunta amfani da su. Sauran sun hada da na manyan na'urori masu kwakwalwa, da na samar da sabbin kayayyaki, da na fannin ba da hidima, da na hada hadar kudi da kasuwanci.

An ce darajar ayyukan da suka samu jarin waje, a jerin ayyukan da aka rattabawa hannu, sun haura na dalar Amurka biliyan 16, ciki hadda na kamfanin Sam Club reshen birnin Shanghai na kasar ta Sin.

Bugu da kari, birnin na Shanghai ya kuma samar da wani dandalin talla, mai kunshe da bayanai daban daban har kimanin 400, masu nasaba da manufofin birnin na zuba jari, da sassan masana'antun birnin 200, da kuma ofisoshi har 3,000. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China