Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai dace ba a hada tallafin Sin da siyasa
2020-03-31 19:52:50        cri
Wasu 'yan siyasar kasashen yamma suna ta shafawa kasar Sin kashin kaji ta hanyar hada matakan da ta dauka da siyasa, yanzu haka yayin da kasar Sin take kokarin tura kayayyakin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19 zuwa ketare domin tallafawa sauran kasashe, wadannan 'yan siyasa sun sake baza jita-jitar, inda suka bayyana cewa, kasar Sin ta yi haka ne domin gindaya masu wani sharadi na siyasa.

A yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi jiya, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta gabatar da tambayarta cewa, ko suna son kada kasar Sin ta kula da yanayin da sauran kasashen duniya ke ciki, kar ta yi kome?

Yanzu annobar COVID-19 tana yaduwa cikin sauri a kasashe da dama dake wajen kasar Sin, kasashen duniya sama da 200 suna fama da annobar, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai fiye da dubu 700, a cikin wadannan kasashen, adadin a Amurka da Italiya ya zarta dubu 100, a don haka ya dace daukacin kasashen duniya su hada kai su dauki matakai tare ba tare da bata lokaci ba domin ganin bayanta, kamar yadda shugabannin kungiyar G20 suka bayyana yayin taron kolinsu.

Hakika a daidai wannan lokaci mai muhimmanci, kasar Sin ta yi kokarin samar da tallafi ga kasashe masu bukata gwargwadon karfinta, kamfanonin kasar ta Sin su ma suna samar da kayayyakin kandagarkin cutar ba dare ba rana, jaridar The Globe and Mail ta kasar Canada ita ma ta bayyana cewa, kasar Sin tana samar da kayayyakin kandagarkin cutar ga kasashen duniya bisa saurin da ba a taba ganin irinsa ba a baya, duk wadannan sun nuna cewa, kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta a matsayinta na babbar kasa, kana ya nuna wa al'ummomin kasa da kasa kirki da soyayya ta Sinawa.

Amma game da hulda mai inganci dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun bayyana cewa, kasar Sin tana samar da tallafin jin kai ne domin kara habaka tasirin siyasarta.

An lura cewa, annobar da take bazuwa cikin sauri a fadin duniya kamar wutar daji, ta sake gaskanta cewa, daukacin bil Adama makomarsu guda daya, babu wata kasa dake iya killace kanta daga wannan masifar, saboda annobar tana shafar daukacin bil Adama, ana sa ran wadannan 'yan siyasar kasashen yamma za su yi watsi da son kai, su kuma daina ci gaba da hada tallafin kasar Sin da batu na siyasa, in ba haka ba, son kai zai haifar musu da mummunar illa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China