Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana gaggauta hadin gwiwar kasa da kasa a fannin ilmin kimiyya da fasaha wajen yaki da COVID-19
2020-03-31 13:55:18        cri

A wannan muhimmin lokaci na yaki da cutar numfashi ta COVID-19 tsakanin kasa da kasa, shugabannin kungiyar G20 sun sanar da kyakkyawar alama, ta yin hadin gwiwa domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a taron koli na musamman na kungiyar G20 mai taken "fuskantar cutar numfashi ta COVID-19" da aka yi a ranar 26 ga wata. Kwanan baya, kasar Sin da kasashen duniya suna gaggauta hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin nazarin allurar rigakafi, da ba da jinya da sauransu, kuma tana samar da taimakon kayayyakin jinya ga kasashen duniya cikin himma da kwazo, lamarin da ya gaggauta hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar.

Kasar Sin tana bin hanyar hadin gwiwar kasa da kasa, tun lokacin da ta fara yin nazari kan allurar riga kafin cutar numfashi ta COVID-19. Mataimakin ministan harkokin kimiyya da fasaha na kasar Sin Xu Nanping, ya bayyana cewa, bayan Sin ta samu jerin kwayoyin dabi'ar cutar, ta gabatar da rahotonta ga kasa da kasa, domin tana fatan fara hadin gwiwar kasa da kasa, wajen nazari kan allurar riga kafi cikin sauri. Yace, a halin yanzu, kasar Sin tana inganta ayyukan nazarin allurar rigakafi ta hanyoyi guda biyar, bisa hadin gwiwa tsakaninta da kasa da kasa.

A lokacin da kasar Sin take dukufa wajen karfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin yin nazari kan allurar rigakafi, tana kuma yin iyakacin kokarinta wajen samar da taimakon kayayyakin jinya ga kasa da kasa.

A safiyar ranar 29 ga wata, an isar da kayayyakin jinya har ton 80 a filin jiragen sama na kasa da kasa na JFK dake birnin New York na kasar Amurka, kana, wannan shi ne taimakon kayayyakin jinya rukuni na farko da Sin ta turawa kasar Amurka daga birnin Shanghai.

Haka kuma, bayan barkewar annobar a kasashen Turai, kasar Sin ta tura tawagogin likitoci da dama, da kayayyakin jinya masu yawa zuwa kasashen da suke fi fama da cutar, kamar kasar Italiya da sauransu.

A kasashen Afirka kuma, a ranar 22 ga wata, an aike da abun rufe hanci da baki, da tufafin kariyar jiki, da akwatunan binciken cutar numfashi ta COVID-19 sama da miliyan 7 zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wadanda asusun taimakon jama'a na Jack Ma, da Asusun taimakon jama'a na Alibaba suka samarwa kasashen Afirka. Yanzu kuma, ana jigilar wadannan kayayyaki zuwa kasashe 54 na nahiyar Afirka.

Cuta wadda ba ta san kan iyakokin kasa da kasa ba, abokiyar gaba ce ta daukacin bil Adama, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yayin taron kungiyar G20. Ya kuma kara da cewa, ana bukatar hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa, domin karfafa aniyarmu ta yaki da cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China