Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta dauki hakikanin mataki domin tabbatar da karfin tattalin arzikin duniya
2020-03-30 20:11:35        cri
Duk da ruwan saman da aka sheka jiya da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a tashar ruwan tekun Zhoushan na birnin Ningbo na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar. Ya zuwa karshen shekarar 2019, adadin kayayyakin da aka jigilar su daga tashar ruwan Zhoushan ya kai tan biliyan 1 da miliyan 120, adadin da babu kamarsa a duniya a cikin shekaru 11 da suka gabata, kafin ziyarar da ya kai tashar, shugaba Xi ya halarci taron kolin musamman na G20 ta kafar bidiyo a yammacin ranar 26 ga wata, inda ya bayyana cewa, yanzu haka ya dace a hada kai domin tabbatar da zaman karkon jerin ayyukan masana'antu da ayyukan samar da kayayyaki. A cikin watanni biyu na farkon bana, adadin kayayyakin da aka jigilar su a tashar ruwan tekun Zhoushan ya kai tan miliyan 163, adadin da ya kai kaso 98 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta dauki hakikanin mataki domin tabbatar da karfin tattalin arzikin duniya.

Yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka kira a ranar 27 ga wata domin tattauna yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu, kasar Sin ta tsai da kudurin farfado da masana'antu da kara habaka kasuwa a kasar, kana ta jaddada cewa, abu mai muhimmanci shi ne kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangarorin tattalin arziki da cinikayya, tare kuma kafa tsarin samar da kayayyaki tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a tabbatar da jigilar kayayyaki a fadin duniya yadda ya kamata.

Yanzu annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa cikin sauri a fadin duniya, kasashe da dama sun rufe layukan zirga-zirgar jiragen sama, a don haka jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa ta gamu da matsala, a irin wannan yanayi, kasar Sin tana ci gaba da kokari matuka domin tabbatar da jigilar kayayyakin ba da kariya domin ganin bayan annobar, ya zuwa ranar 26 ga wata, gaba daya hukumar zirga-zirgar jiragen saman kasar Sin ta tura jiragen sama 23 domin jigilar kayayyakin ba da kariya na yakar annobar, kayayyakin da kasar Sin ta yi jigilar su sun kai tan sama da 400.

A yayin taron kolin shugabannin kasashen mambobin G20 da aka kira ta kafar bidiyo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara samar da magunguna da kayayyakin yau da kullum da kayayyakin ba da kariya ga kasuwar duniya, ta yadda za a taimakawa al'ummomin kasa da kasa da suke bukata.

Kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya rubuta a cikin wasikar da ya aika wa shugabannin G20, yanzu ya dace a hada kai a maimakon nuna kyama, kamata ya yi kasashen duniya su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu domin kare lafiyar daukacin bil Adama.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China