Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararren Namibia: Ya dace Afrika ta yi koyi daga kasar Sin a yaki da fatara
2020-03-30 10:34:14        cri
Wani kwararren masanin tattalin arziki a kasar Namibia ya ce, ya kamata kasar Namibiya da sauran kasashen Afrika su yi koyi daga kasar Sin wajen aikin yaki da fatara musamman a tsakanin mazauna karkara bayan fuskantar annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Omu Kakujaha-Matundu, wani masanin tattalin arziki dake jami'ar kasar Namibia, ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su samu kwarin gwiwa game da yadda kasar Sin take yaki da fatara.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance dadaddiyar aminiya ga kasashen Afrika, amma har yanzu akwai muhimman darrusa da ya kamata shugabannin Afrika su koya daga kasar Sin game da tsara manufofin yaki da fatara kamar yadda kasar Sin take yi. Yana da muhimmanci ga kasashen da su bi irin hanyoyin da kasar Sin take bi wajen yakar talauci a tsakanin al'ummarta marasa galihu ta hanyar raya aikin gona. Ya kamata shugabannin Afrika su koyi darasi daga wadannan manufofi kuma su kaucewa tsara manufofin da za su biya bukatunsu na kashin kai.

Masanin tattalin arzikin ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta yi fice wajen yaki da fatara da kuma kyautata zaman rayuwar talakawa masu karamin karfi. Muddin shugabannin suka yi koyi da kasar Sin wajen tinkarar kalubalolin tattalin arziki da inganta rayuwar matalauta da yaki da rashawa, Afrika za ta samu gagarumin ci gaba. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China