Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fox Ya Sallami Trish Regan
2020-03-28 23:01:34        cri

Kafar Fox Business Network ta Amurka ta sallami ma'aikaciyarta Trish Regan, wadda ta taba yin muhawara da Liu Xin, takwararta ta kafar CGTN ta kasar Sin. A labarin da jaridar New York Times ta wallafa, an ce, FOX ya dakatar da shirinta a ranar 13, sai kuma ya zuwa jiya, ya sanar da sallamarta daga aiki.

A shirinta na wannan wata, Trish Regan ta ce, jam'iyyar Democrat na dora wa shugaba Trump laifin yin sakaci da aiki wajen shawo kan cutar Covid-19, kuma tana neman lalata sunan shugaban. Sharhin da ya samu suka sosai.

A game da yadda aka sallame ta, malama Liu Xin, mai gabatar da shirye-shirye a kafar CGTN, ta bayyana takaicinta da cewa, "Kasancewarta dalibar da ta karanta ilmin tarihi a jami'ar Columbia, mun yi zaton kwarewarta ta wuce haka, da fatan lamarin zai sa ta gane cewa, gaskiya ba ta buya"

Mara bayan wata jam'iyyar siyasa ya zama al'ada ga kafofin yada labarai na Amurka, kuma daga cikinsu, kafar Fox ta shahara da tsayawa tare da shugaba Donald Trump. Sai dai yayin da yawan masu harbuwa da cutar Covid-19 ya zarce dubu 100 a Amurka, masu gabatar da shirye-shirye na FOX wadanda a baya suka yi kokarin boye illolin da cutar ke haifarwa, yanzu kuma suna gyara bakinsu. Amma malama Trish daga nata bangaren ta tsaya kan matsayinta, lamarin da ya bata ran al'ummar kasar Amurka da ke yaki da cutar. Domin matsin da al'ummar kasa da ma masu bada tallar kayansu a kafar suka yi, ba yadda Fox ya iya, sai dai ya sallame ta.

Kafofin yada labarai na Amurka sun sha yin biris da nauyin da ke wuyansu, har ma sun zama kayan aiki na gwagwarmayyar siyasa. A halin da ake ciki na fuskantar cutar Covid-19, kamata ya yi kafofin yada labarai su sauke nauyinsu na hada karfin gwamnati da al'umma, sai dai a Amurka, hakan ya zama labari.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China