Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tibet ta yi bikin ranar samun 'yanci daga tsarin ci da gumin matalauta
2020-03-28 21:50:51        cri
Qizhala, shugaban gwamnatin yankin Tibet mai cin gashin kansa, na kudu maso yammacin kasar Sin, ya gabatar da wani jawabi ta talabijin a yau Asabar, domin tunawa da ranar samun 'yancin yankin daga tsarin ci da gumin matalauta

Shekaru 61 da suka gabata, aka 'yantar da sama da mutane miliyan 1 ko kaso 90 na al'ummar yankin a wancan lokaci, daga tsarin na ci da gumi.

A cewar shugaban, manyan sauye-sauyen da aka samu a Tibet cikin gomman shekarun da suka gabata, sun nuna karfin tsarin gurguzu mai halayyar kasar Sin, da kaunar da kasa ke wa al'ummarta da kuma yadda makomar yankin ke alaka ta kut da kut da kasar.

Alkaluman GDP na yankin ya tashi zuwa yuan biliyan 160, kwatankwacin dala biliyan 22.7 a bara, wanda ya ninka kan na shekarar 1951 har sau 206.

Yankin Tibet ya yi nasarar fatattakar talauci baki daya, inda dukkan yankunansa suka fita daga cikin jerin matalauta. Matsakaicin matakin rayuwar al'ummar Tibet ya tashi zuwa shekaru 70.6 akan shekaru 35.5 da yake a shekarar 1959. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China