Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin Amurka na zartar da dokar dake da alaka da Taiwan zai janyowa sauran kasashe da ma kanta lahani
2020-03-28 20:51:33        cri

A ranar 26 ga wata bisa agogon wurin, Amurka ta zartar da dokar kare dangantakar Taiwan da kawayenta ta 2019, inda aka hana sauran kasashe kulla huldar diplomasiyya da Sin, da taimakawa Taiwan wajen habaka dangantakar dake tsakaninta da kasa da kasa, matakin dake zaman tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin kiri da muzu.

Wannan dokar da ta shafi Taiwan, ta sabawa manufar Sin daya tak a duniya, da hadaddiyar sanarwa uku dake tsakanin Sin da Amurka, da kuma dokar kasa da kasa da babbar ka'idar kasa da kasa, ta kuma nuna alama ta kuskure ga 'yan awaren Taiwan, da illata hadin kan kasa da kasa na yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Yanzu haka, Amurka ta kasance wadda ta fi yawan masu fama da cutar COVID-19 a duniya. A wannan muhimmin lokaci, maimakon kasar ta kula da tsaron lafiyar jama'arta, sai take bada muhimmanci kan zartar da wannan dokar dake da alaka da Taiwan, wadda ke tayar da kiyayya. Ta hakan za a gano dalilin da ya sa Amurka dake kan gaba a fannin likitanci a duniya ta kara rasa dama mai kyau ta kandagarkin annobar.

Ya zuwa yanzu, akwai kasashe 180 da suka kulla huldar diplomasiyya da Sin. Amurka ta kara amfani da batun Taiwan da nufin lahanta halin yakar annoba ta hanyar hadin kan kasa da kasa, matakin da ya kawo cikas ga hadin kan kasashen Sin da Amurka na yakar cutar, wanda kuma ya zama rashin daukar nauyin dake wuyanta na kula da lafiyar jama'arta.

Batun Taiwan na shafar babbar moriyar kasar Sin, manufar kasar Sin daya kacal, babban tushe ne a siyasance kan dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, ita ce kuma ra'ayin bai daya da kasashen duniya suka cimma. A gargadi bangaren Amurka da ya kawar da kuskuren da ya yi, da daina amfani da hujjar dokar dake da alaka da Taiwan, da daina hana kasashe daban daban ciyar da dangantakar dake tsakaninsu da Sin gaba, in ba haka ba, kasar Sin za ta mayar da martanin da ya dace. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China