Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar The Lancet ta jaddada muhimmancin hadin kan kasa da kasa da daukar darasi daga kasar Sin
2020-03-28 17:12:46        cri
Jaridar The Lancet mai wallafa batutuwan kiwon lafiya, ta wallafa wata mukala a jiya, mai taken " Cutar COVID-19: daukar darasi daga matakan da aka dauka", inda ta bukaci kasashen duniya su gaggauta shawo kan annobar bisa matakai masu inganci, tare da jaddada muhimmancin daukar darasi daga kasar Sin da kuma hadin kan kasa da kasa.

Mukalar ta kuma soki wasu kasashe, musammam Birtaniya da Amurka da Sweden, da jan kafa wajen tunkarar cutar a matakanta na farko. Inda Ta ce "mummunan ra'ayin shugabannin wasu kasashe ya kai ga asarar rayukan mutane da dama".

Ta kuma jaddada cewa, abu ne mai matukar muhimmanci, fahimtar yadda Sin za ta iya janye matakanta masu tsauri. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China