Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su hada kai don tinkarar cutar COVID-19
2020-03-27 21:51:41        cri

"Bisa yanayin da ake ciki ne, ya kamata kasashen Sin da Amurka su hada gwiwa don yakar annobar COVID-19." Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bayyana hakan a yau Jumma'a, a zantawarsa ta wayar tarho da shugaban kasar Amurka Donald Trump.

Wannan ne karo na biyu, da shugabannin kasashen biyu suka tattauna batun yanayin cutar numfashi ta COVID-19 a cikin rana daya. Kafin hakan kuma, a daren ranar 26 ga wata, shugabannin kungiyar G20 a karon farko suka shirya taron kolin na musamman game da batun yanayin annobar, wanda ya samu halartar shugabannin Sin da Amurka.

Abun lura a nan shi ne, shugabannin biyu sun yi zantawar har sau biyu ke nan, bisa yanayin gaggawa da kasar Amurka ke ciki na yakar annobar. An ce ya zuwa yanzu, kasar ta riga ta kasance kan gaba, cikin kasashen da cutar ta fi kamari a duniya, don haka, hana yaduwar cutar ya zama bukatar gaggawa ta kasar Amurka. Baya ga haka, a yayin da ake tinkarar annobar, wasu 'yan siyasar kasar Amurka suna ta mayar da yanayin annobar a matsayin maganar siyasa, da neman shafa wa kasar Sin kashin kaji, wadanda suka lahanta kokarin da ake na neman hadin kan kasashen biyu game da yakar cutar, kana da kawo cikas ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da ayyukan yakar annobar.

A yayin zantawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, tun bayan bullar cutar COVID-19, kasar Sin ba ta boye komai ba, wajen more fasahohin da ta samu, a fannin kandagarki da shawo kan cutar, tana kuma yin namijin kokarinta, don nuna goyon baya da taimakawa kasashen dake bukata, kana kasar za ta ci gaba da yin hakan.

Baya ga haka, Xi Jinping ya bayyana fatansa, na ganin bangarori daban daban za su karfafa hadin kai da daidaito, don tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron kolin na musamman na G20. A matsayinsu na manyan kasashe a fannin tattalin arziki a duniya, ya kamata kasashen Sin da Amurka su ba da misali mai amfani a wannan fannin.

Game da tambayar da Donald Trump ya yi masa, Xi Jinping ya yi bayani sosai kan matakan da kasar Sin ta dauka na yakar annobar, ya kuma bayyana cewa, yana fahimtar mawuyacin halin da Amurka ke ciki, kana kasarsa za ta ci gaba da more bayanai, da fasahohin da ta samu, tare kuma da nuna goyon baya gwargwadon karfinta.

A nasa bangaren, Donald Trump ya nuna yabo kan ra'ayi da shawarar da Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron kolin na G20, ya kuma bayyana cewa, shi kansa zai kula da ayyukan dake shafar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu wajen yakar annobar. Baya ga haka, ya yi godiya ga kasar Sin kan kayayyakin likitanci da ta samarwa kasar Amurka. A cewarsa, kasar Amurka za ta kiyaye tsaron Sinawa dake kasar, ciki har da daliban Sin dake karatu a kasar. Irin ra'ayin da ya bayyana, ya samar da wani sharadi mai kyau ga hadin kai a tsakanin kasashen biyu, wajen kandagarkin cutar.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China