Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarar kasar Sin ta baiwa duk duniya kwarin gwiwar yakar COVID-19
2020-03-27 15:23:43        cri

Daren jiya Alhamis agogon Beijing, shugaba Xi Jinping ya halarci taron kolin G20 ta kafar bidiyo kan COVID-19, inda ya ba da shawarar cewa: al'ummar duniya na bukatar kwarin gwiwa da hadin kai matuka a halin yanzu. Ya ce kamata ya yi a kara hadin kan kasa da kasa da daukar matakai masu inganci tare, don cimma nasarar yakar wannan mumunar cuta mai tsanani.

Shugabannin kasashe mafi karfin tattalin arziki da kungiyoyin kasa da kasa sun kira taro ta kafar bidiyo karo na farko a gabar yaduwar wannan cuta a duniya, inda suke da buri iri daya, wato tattauna manufofi da matakan da za a dauka, da ingiza hadin kan kasa da kasa don tinkarar cutar tare da ba da tabbaci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. A cikin wannan taro na musamman, Shugaba Xi ya ba da jawabi don gabatar da fasahohi da ci gaban da Sin take samu wajen yaki da cutar, kuma ya gode sosai da taimakon da aka baiwa kasar Sin a mawuyancin halin da kasar ke ciki, tare da gabatar da manufa irin ta kasar Sin wajen yakar cutar tare da ba da shawarar kara hadin kan kasa da kasa don yakar cutar da ba da tabbaci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Shugaba Xi ya ba da shawarwari guda hudu a yayin taron, wato bayyana niyyar magance cutar a duk fadin duniya, da hadin kan kasa da kasa don yaki da kandagarkin cutar da kuma goyon bayan taimakon da kungiyoyin kasa da kasa suke bayarwa, sannan da kara daidaita manufofin gwamnatocin kasa da kasa kan tattalin arziki.

Ko da yake wannan cuta mai tsanani na bulla a duk fadin duniya, cutar ta rage yaduwa a kasar Sin, matakin da ya nuna cewa, ana iya hana yaduwarta muddin ana daukar manufofi masu dacewa da daukar matakai masu inganci da kara hadin kai. Abin lura shi ne, taron ya ba da wata sanarwa cewa, kamata ya yi bangarori daban-daban su yi iyakacin kokari wajen ceton rayuwar jama'a, da kara kwarin gwiwar jama'a da farfado da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma kawar da rage illar da cutar ke kawowa cinikin duniya da sha'anin samar da kayayyaki, da kuma baiwa sauran kasashe taimako idan suka bukata da kuma daidaita tsare-tsaren kiwon lafiya da na kudi na kasa da kasa. Ana iya ganin cewa, shawarar kasar Sin ya samu karbuwa a taron, har an shigar da su cikin sanarwar da aka bayar.

Cutar makiyin dukkanin Bil Adama ne, ba wata kasa da za ta iya kare kanta ita kadai, kasashen duniya na bukatar hadin kansu kwarai da gaske a maimakon shafawa sauran kasashe bakin fenti, matakin da ba zai yi wani amfani ba sai haifar da illa. Kamar yadda wasu masana ke bayyana cewa, ana bukatar tunanin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da Sin ta gabatar matuka a daidai wannan lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China