Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron ministocin harkokin wajen G7 ya gaza cimma matsayar Amurka da Turai
2020-03-26 13:56:14        cri

Taron ministocin harkokin wajen kungiyar G7 da aka yi a jiya Laraba, ya mai da hankali ne kan yadda za a dauki matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen duniya, kuma ministocin harkokin wajen da suka halarci taron sun yarda su hada kai gwiwa wajen hana yaduwar cutar.

Kafar yada labarai ta CNN ta kasar Amurka ta ruwaito a jiya Laraba cewa, a yayin taron, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi kokarin shigar da kalmar "kwayar cutar Wuhan" cikin sanarwar hadin gwiwa ta mambobin kungiyar G7, amma, wasu mambobin kungiyar sun ki amincewa, wannan ya sa, ba a fitar da sanarwar hadin gwiwar wannan taro ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China