Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani birni a Sin ya kaddamar da manhajar kwarmata masu aikata laifin ta'ammali da dabbobi daji
2020-03-26 10:42:56        cri

Birnin Hangzhou dake gabashin lardin Zhejiang na kasar Sin a ranar Laraba ya kaddamar da wata manhaja ta wayar hannu domin gano masu aikata laifukan mu'amala da dabbobin daji da aka haramta ta'ammali dasu.

Mazauna birnin za su iya aikewa da rahotanni kwarmata masu farautar dabbobin dajin ko kuma cinikinsu ta hanyar sakaye sunayensu, da kuma masu sayen nau'in dabbobin daji ta wayoyin hannu da cikakkun bayanai game da wuraren da suke da zama, da hotuna ko kuma bidiyonsu, a cewar hukumar gudanarwar birnin Hangzhou, an kirkiri manhanjar ne ta asusun Alipay, daya daga cikin shafukan biyan kudade ta intanet mafi shahara a kasar Sin a helkwatarsa dake birnin Hangzhou.

Haka zalika, jama'a za su iya kwarmata rahoton masu aikata laifukan ta'ammali da dabbobin dajin ta wasu layukan waya na musamman da aka tanada.

Wannan mataki ya biyo bayan dokar da majalisar kasar Sin ta zartas ne tun a ranar 24 ga watan Fabrairu inda ta haramta dukkan nau'in ciniki ko amfani da dabbobin daji a duk fadin kasar domin kiyaye lafiyar jama'ar kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China