Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce zai daina furta "Cutar kasar Sin"
2020-03-25 21:03:59        cri
A baya bayan nan, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana wa manema labarai cewa, ya yanke shawarar daina ambatar cutar COVID-19 da kalmar "cutar kasar Sin".

A game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin na matukar adawa da kalaman da suka bata sunanta, kuma fatanta shi ne Amurka za ta hada kai da kasar Sin, da ma sauran kasashen duniya, don tinkarar cutar COVID-19, tare da kuma matakan kare lafiyar al'ummar duniya baki daya. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China