Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakamakon gwaji na nuna mataimakin shugaban Najeriya ba ya dauke da cutar COVID-19
2020-03-25 20:54:59        cri

Sakamakon gwajin da aka yiwa mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya nuna ba ya dauke da kwayar cutar numfashi ta COVID-19.

A cewar kakakin mataimakin shugaban kasar, a gabar da ake cikin darurar yanayin da Mr. Osinbajo yake ciki, an gano cewa shi da sauran mukarrabansa, wadanda aka yiwa gwajin ba sa dauke da cutar.

Tun farkon makon nan ne dai mataimakin shugaban Najeriyar ya kebe kan sa, kamar yadda tsarin dakile yaduwar wannan cuta ya tanada, bayan da Mr. Osimbajo ya yi cudanya da wani babban jami'i a fadar shugaban kasa, wanda aka tabbatar ya kamu da cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China