Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan guraben aikin da aka samar bisa shirin da aka tsara ya zarce dubu 210
2020-03-23 19:19:30        cri

Kwanaki sama da 20 ke nan, tun bayan da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), da ma sauran hukumomin kasar suka hada kai, wajen kaddamar da shirin daukar ma'aikata ta yanar gizo, wanda ya janyo manyan kamfanonin gwamnati, da ma shahararrun kamfanoni masu zaman kansu na kasar, da ma sauran sassan al'umma kimanin 3200, wanda kuma kawo yanzu, ya samar da guraben aiki sama da dubu 210, ga daliban jami'o'i da za su kammala karatunsu a wannan shekara.

Dangane da matsalar karancin 'yan kwadago a lokacin annobar cutar COVID-19, da ma yadda 'yan kwadago suka rasa samun kafofin neman aiki, CMG ya kaddamar da shirin bisa manhajarsa ta Yangshipin, tun daga ranar 2 ga wata. Kuma cikin kwanaki 20 da suka wuce, gaba daya an gudanar da taruka 31 ta yanar gizo, don kamfanonin da suke neman daukar ma'aikata su bayyana manufofinsu.

A nasu bangaren kuma, 'yan kwadago sun yi ta halartar tarukan da aka shirya ta yanar gizo, don neman damar aiki. Gaba daya kuma an samu takardun tarihin 'yan kwadagon sama da dubu 750. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China