Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole ne Amurka ta baiwa duniya amsa kan tambayoyi 3 game da cutar COVID-19
2020-03-22 22:06:12        cri
A kwanakin nan ne ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba wasu 'yan siyasar Amurka sun kira "coronavirus" a matsayin "kwayar cutar China", abun da ya jawo kakkausar suka daga kasa da kasa 'Yar jaridar Sky News ta kasar Burtaniya, Amanda Walker ta bayyana cewa, idan miliyoyin mutanen Amurka sun rasa rayukansu sakamakon annobar cutar COVID-19, dole ne a dorawa shugaba Trump laifin. Amma ya kira "kwayar cutar China" maimakon "coronavirus" ne domin gudun zargin da aka yi masa.

Nemo asalin wani nau'in kwayar cuta, batu ne da ya shafi kimiyya, wanda ke bukatar ingantattun shaidu. Dr. Giuseppe Remuzzi, babban daraktan cibiyar nazarin ilimin magunguna ta Mario Negri ta kasar Italiya ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne an samu bullar cutar huhun da ake zargin cutar COVID-19 ce tun a watannin Nuwamba da Disambar bara a kasar. A sabili da haka, yana tsammanin cewa, kafin a lura da bayyanar annobar cutar COVID-19 a kasar Sin, kwayar cutar ta fara bazuwa a yankin Lombardia dake arewacin kasar Italiya. Shi ma a nasa bangaren, firaministan kasar Australiya Scott Morrison ya bayyana cewa, kimanin kaso 80% daga cikin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar, sun shigo kasar ne daga sauran sassan duniya, ko kuma sun taba yin mu'amala kai-tsaye da wadanda suka shigo kasar daga ketare, kana, akasarinsu daga Amurka ne.

 

 

Yanzu ana kara nuna shakkun ga kasar Amurka, inda kamata ya yi gwamnatin kasar ta baiwa duk fadin duniya amsarta ga wasu muhimman tambayoyi uku kan annobar cutar.

Na farko, bisa alkaluman da cibiyar takaita cututtuka masu yaduwa ta Amurka ta bayar, akwai mutane sama da miliyan 30 wadanda suka kamu da cutar mura wadda ta barke a watan Satumbar shekara ta 2019 a Amurka, kana adadin mutanen da suka mutu ya zarce dubu 20. Shugaban cibiyar Robert Redfield ya bayyana a kwanan baya cewa, daga cikin mutanen da suka mutu, akwai wasu wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ba mura ba. To, tambayar a nan ita ce, daga cikin mutane sama da dubu 20 da suka rasa rayukansu, mutane nawa ne suka mutu sakamakon cutar COVID-19? Shin Amurka tana yunkurin juya gaskiyar halin da ake ciki na COVID-19 bisa hujjar cutar mura ne?

Tambaya ta biyu ita ce me ya sa a watan Yulin shekarar 2019, ba zato ba tsammani Amurka ta rufe cibiyar Fort Detrick ta kirkiro makaman amfani da kwayoyin halitta da sinadarai masu guba dake jihar Maryland ta kasar? Cibiyar da ta kasance mafi girma ta nazarin makamai na sojojin kasar. Ba da jimawa ba ta rufe cibiyar, sai aka gano bullar cututtukan ciwon huhu kasar. Kusan a lokaci daya ne kuma, cutar H1N1 ta bulla a kasar. Daga baya a watan Oktoban shekarar bara, hukumomi da dama na kasar ta Amurka sun shirya atisaye mai lakabin "Event 201" don tinkarar barkewar cuta a fadin duniya. A watan Disamban bara kuma, an fara gano bullar cutar COVID-19 a birnin Wuhan, sai kuma ya zuwa watan Fabrairun wannan shekara, cutar ta barke a sassan duniya da dama.

 

 


Tambaya ta uku kuma ita ce, me ya sa a tsakiyar watan Fabrairun bana, gwamnatin kasar Amurka ta nuna halin ko-in-kula game da halin da kasar ke ciki dangane da yaduwar cutar COVID-19, a yayin da jami'an kasar da dama dake cikin kwamitin leken asiri na majalisar dattawan kasar suka sayar da hannayen jarinsu da kudinsu ya kai sama da miliyan a lokacin? Ko sun boye ainihin halin da ake ciki ga al'umma? Ko a ganinsu kudin jari ya fi rayukan al'umma ne?


 

 

Ya zuwa jiya Asabar da dare, agogon kasar, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya kai 26747, a yayin da yawan wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar ya kai 340. A mawuyacin halin da ake ciki, kamar yadda Yuval Noah Harari ya bayyana cewa, wasu 'yan siyasar Amurka basu taba daukar nauyin dake bisa kansu ba, basu taba amincewa da kuskuren da suka tafka ba. Kullum suna dora nasara a kansu a yayin da suke dora laifi kan saura." (Murtala Zhang, Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China