Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Owei Lakemfa: A daina bata sunan sauran kasashe yayin da ake dakile cutar COVID-19 a duniya
2020-03-22 20:23:23        cri

Jiya Asabar, wani masani mai suna Owei Lakemfa ya wallafa wani sharhi a jaridar Vanguard ta Najeriya, mai taken "Makaman kare-dangi, wahalar da dan Adam ba zai iya jurewa ba", inda ya ce, dan Adam na fuskantar babbar barazana daga kwayoyin cuta kamar COVID-19, ya zama dole a dakatar da duk wata aika-aika ta sanya batun siyasa da bata sunan sauran kasashe a yayin da ake kokarin ganin bayan cutar. Sharhin ya kuma jaddada cewa, ba za'a iya haye wahalhalun ba sai dai kawai kasa da kasa su yi cude-ni-in-cude-ka.

A cikin sharhin, Mista Owei Lakemfa ya ce, yin amfani da annobar cutar COVID-19 domin bata sunan wata kasa zai yi babbar illa ga daukacin al'ummar duniya, inda ya yi kira ga shugaba Trump na Amurka ya dakatar da kira "COVID-19" a matsayin "kwayar cutar China". Ya ce ya kamata kasa da kasa su zama tsintsiya madaurinki daya domin tinkarar annobar, da kare duk duniyarmu cikin hadin-gwiwa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China