Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a samu rahoton sabbin wadanda suka kamu da COVID-19 a Wuhan ba kwanaki 4 a jere
2020-03-22 17:55:04        cri
Ba a samu sabbin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta (COVID-19) a birnin Wuhan a jiya Asabar ba, hakan ya tabbatar da cewa an samu kwanaki hudu ke nan a jere ba tare da samun rahoton sabbin mutanen da suka kamu da cutar a birnin da cutar tafi kamari ba, bayan an shafe watanni ana kokarin dakile kwayar cutar.

Hukumar lafiyar kasar Sin ta kuma sanar a yau Lahadi cewa ta samu rahoton sabbin mutane 46 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a duk fadin kasar a ranar Asabar, sai dai 45 daga cikinsu daga kasashen ketare suka shigo da cutar.(Ahmad Inuwa Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China