Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar kwararrun likitocin Sin sun isa kasar Serbia don yakar COVID-19
2020-03-22 16:59:28        cri
Da yammacin jiya Asabar tawagar kwararrun jami'an kiwon lafiyar kasar Sin ta isa babban birnin kasar Serbia domin taimakawa kasar yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 yayin da kasar ta dukufa aikin dakile annobar.

Tawagar kwararrun mai kunshe da mambobi shida ta samu kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic, da ministan lafiyar kasar Zlatibor Loncar, da ministan tsaron kasar Aleksandar Vulin da kuma sauran manyan jami'an gwamnatin kasar a filin jirgin saman birnin Belgrade.

Likitocin na kasar Sin, sun kunshi kwararru a fannonin dakile yaduwar cututtuka wato (IDP), da kwararrun masana kula da cuta mai tsanani (PCCM), sun tafi tare da kayayyakin kiwon lafiya da ake tsananin bukata a kasar ta Serbia, ya zuwa yanzu, an samu wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 kimanin 171 a kasar kana da mutuwar mutum guda.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China