Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Namibiya za ta yi amfani da maganin gargajiyar kasar Sin wajen magance COVID-19
2020-03-20 19:41:58        cri
Babban darektan ma'aikatar lafiya da jin dadin jama'a na kasar Namibiya, Ben Nangombe, ya bayyana aniyar kasarsa ta rungumar maganin gargajiyar kasar Sin wajen yaki da barkewar cutar numfashi ta COVID-19.

Jami'in wanda ya bayyana haka yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya ce, kasarsa za ta koya tare da maraba da kyawawan fasashohin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yaki da wannan annoba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China