Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har kullum Sin na maraba da 'yan jaridar kasashen waje in ji Geng Shuang
2020-03-19 10:05:48        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce har kullum kasar Sin na maraba da 'yan jarida daga kasashen ketare, da su shigo kasar domin gudanar da ayyukansu bisa doka da bin ka'idojin kasa.

Geng Shuang, wanda ke wannan tsokaci yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya Laraba, game da matakan da Sin ke dauka a matsayin martani ga Amurka, don gane da matsin lamba da take yiwa 'yan jaridar Sin masu aiki a Amurka, ya ce Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayi, da taimako ga 'yan jarida dake aikinsu bisa doka.

Mr. Geng ya ce matakan na Sin sun zama wajibi, kuma ramuwa ce ga irin cusgunawar da ake yiwa kafofin watsa labaran na Sin a Amurka, don haka ko shakka babu, hakan bai sauya matsayin Sin na aiwatar da manufofin bude kofarta ga ketare a nan gaba ba.

Game da ko wannan mataki zai iya yin tasiri ga matakan da Sin ke dauka game da samar da bayanai, don gane da yaki da cutar COVID-19? Geng ya ce Sin na aiwatar da cikakkun matakai masu inganci, tun bayan barkewar annobar cutar a bude, cikin mutunci, ta yadda za a kai ga cimma nasarorin da aka sanya gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China