Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Ta Mai Da Martani Ga Kafofin Watsa Labaran Amurka Yadda Ya Kamata
2020-03-18 20:23:29        cri

Yau Laraba, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da matakai guda uku domin mai da martani ga kasar Amurka dangane da tarnakin da ta kakaba wa kafofin watsa labaran kasarta dake Amurka. Wannan ba abin mamaki ba ne, a lokacin da kasar Amurka ta kori 'yan jaridun kasar Sin tare da kakaba wa kafofin watsa labaran kasar Sin tarnaki, kasar Sin ta jaddada cewa, tana da ikon mai da martani tare da daukar matakai.

A shekarun baya bayan nan, gwamnatin Amurka na ci gaba da kakaba wasu tarnaki ga kafofin watsa labaran kasar Sin. Misali, ta tsara manufar nuna bambanci kan ba da izinin biza ga 'yan jaridun kasar Sin, tun daga shekarar 2018, ya zuwa yanzu, gaba daya kasar Amurka ta ki ba da izinin biza ga 'yan jaridun kasar Sin sama da 30, kuma akwai zaunannun 'yan jaridu guda 9 da ba su iya sake shiga kasar Amurka ba bayan suka tashi daga kasar.

Kasar Amurka ce ta fara sanya tarnaki ga kafofin watsa labarai na kasar Sin, don haka, ita ma kasar Sin babu sauran zabi illa ta mai da martani domin kare 'yancinta.

Idan muka kalli tarnakin da kasar Amurka ta kakaba wa kafofin watsa labarai na kasar Sin, za mu fahimci cewa, 'yancin labarai ya zama babbar kariyar da kasar Amurka ta alfanu da shi, tana kuma musgunawa kafofin watsa labaran kasar Sin bisa tunaninta na yakin cacar baka da nuna bambanci ga kasar Sin.

Amma ko kasar Amurka za ta karawa kanta karfi ta hanyar matsa wa sauran kasashe lamba? Dangane da wannan batu, masanin harkokin kasa da kasa na kasar Faransa, kana wanda ya kirkiro dandalin tattaunawar kasashen Sin da Turai David Gosset ya bayyana cewa, hakan ba ya nuna karfin kasar Amurka ba ne. A hannu guda ya nuna raunin kasar. Sabo da kasa mai karfi da hadin gwiwa ba za ta aikata irin wannan laifi ga kafofin watsa labarai na kasar Sin ba.

Kuma tarnakin da kasar Amurka ta kakaba wa kafofin watsa labarai na kasar Sin, zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya dace kasar Amurka da gaggauta dakatar da irin wadannan halaye da take dauka, sabo da martanin da kasar Sin ta mayar mata ba wasa ba ne, idan kasar Amurka ta ci gaba da aikata irin wannan kuskure, tabbas kasar Sin za ta kara mayar mata martani. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China