Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar hasashen yanayi a Tanzaniya ta yi gargadin samun mamakon ruwan sama a shiyyo 9 na kasar
2020-03-18 11:29:25        cri

A ranar Talata hukumar hasashen yanayi ta kasar Tanzaniya ta sake sabunta gargadinta game da yiwuwar barna da za'a iya fuskanta a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake tsammanin samu a shiyyo tara na kasar.

A bisa hasashenta na baya bayan nan, hukumar hasashen ruwan sama ta kasar Tanzania (TMA), ta ce ana tsammanin za'a fara sheka ruwan saman ne tun daga ranar Talata a yankunan Rukwa, Mbeya, Songwe, Njombe, Iringa, Morogoro, Ruvuma, Mtwara da yankin Lindi.

Hukumar TMA ta ce, ana tsammanin ruwan saman zai iya lalata wasu muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da gine gine a wasu daga cikin shiyyoyin, ta kara da cewa, akwai yiwuwar wasu gidaje da gonaki za su iya salwanta a sanadiyyar ambaliyar ruwa.

Hukumar hasashen yanayin ta ce mai yiwuwa ne a samu katsewar harkokin sufuri, da hada hadar kasuwanci da harkokin yau da kullum a wasu shiyyoyin kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China