Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da samun ci gaba
2020-03-18 11:01:24        cri

Kwanan baya jagoran kamfanin APPLE na Amurka Tim Cook, ya fitar da wata sanarwa, inda ya sanar da cewa, za a ci gaba da rufe kantunan kamfaninsa dake wajen kasar Sin, har zuwa ranar 27 ga wata, kuma za a kira babban taronsa na WWDC ta yanar gizo a watan Yuni mai zuwa, domin rage hadarin bazuwar kwayar cutar numfashi ta COVID-19.

Cook yana mai cewa, yanzu haka kasar Sin ta riga ta cimma burin kayyade bazuwar kwayar cutar, a don haka an sake bude kantunan kamfanin a fadin kasar, lamarin da ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana farfadowa cikin sauri.

Duk da cewa, kasar Sin tana shan wahalar yaduwar annobar cutar COVID-19 a farkon bana, amma tattalin arzikinta zai ci gaba da samun bunkasuwa, hakika bayan aukuwar annobar, hukumomin kudin kasar Sin, sun samar da goyon bayan kudin da yawansa ya kai RMB yuan sama da biliyan 100, tare kuma da fitar da manufofin rangwame domin taimakawa kamfanonin kasar. A sa'i daya kuma, jarin da aka zuba a kasar, shi ma yana karuwa, musamman ma a bangaren tattalin arziki ta yanar gizo.

Abu mai bakanta rai shi ne, yanzu annobar tana bazuwa cikin sauri a sauran kasashen dake wajen kasar Sin, lamarin da shi ma ya kawo hadari ga tattalin arzikin kasar Sin, amma kasar Sin tana cike da imani kan makomar tattalin arzikinta, saboda har kullum tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba ta hanyar dakile wahalhalu iri daban daban, kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana, kasar Sin za ta dakile annobar, kuma za ta maido da tsarin tattalin arzikin ta yadda ya kamata, lamarin ba ma kawai zai amfani al'ummun kasar Sin ba, har ma zai taka rawa wajen ci gaban duk duniya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China