Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malam Song Tianzhu ya fita daga kangin talauci
2020-03-20 09:25:20        cri

 

 

 

Malam Song Tianzhu ke nan 'yar kabilar Zang da ke rayuwa a gundumar Tianzhu mai zaman kanta ta kabilar Zang da ke lardin Gansu na kasar Sin, gundumar da a baya ta kasance gundumar da ke fama da talauci. A shekarar 2013, malam Song Tianzhu ya yanke shawarar kiwon shanu da tumaki bisa rancen kudin da aka samar masa na tallafawa masu fama da talauci, daga nan kuma, sai shanu da tumaki da yake kiwo suka yi ta karuwa, kuma kudin shigarsa ma sai karuwa yake yi, har ma ya hada gwiwa da sauran mazauna kauyen, don su habaka wannan aiki. A farkon bana, gundumar Tianzhu ta fid da kanta daga kangin talauci, kuma malam Song Tianzhu ma ya shahara a kauyensa wajen saukaka fatara.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China