Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin na ba da taimakon samar da guraben aikin yi sama da dubu 100
2020-03-16 14:21:18        cri

Babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG, tare da hadin gwiwar rukunin raya kasa da zuba jari ta kasar, da kuma kwamitin kula da kadarorin kasa karkashin majalissar gudanarwar kasar Sin, sun kaddamar da shirin samar da guraben aikin yi ta yanar gizo daga ranar 2 ga wata.

Kamfanoni da dama sun shiga wannan shiri, inda masu neman aikin yi ke nuna himma da gwazo matuka don neman samun dama. Ya zuwa yanzu dai, kamfanoni mallakar gwamnati da kuma shahararrun kamfanoni masu zaman kansu, sun gudanar da taruka 18 ta yanar gizo don daukar ma'aikatan aiki, tare da samar da guranben aikin yi fiye da dubu 100, kana yawan kamfanonin da suka yi rajista cikin wannan shiri ya kai kimanin 2500. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China