Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yakin Hadin Gwiwa: Yadda AKe Yakar COVID-19 A Wuhan
2020-03-15 21:52:09        cri

Bayan karbar sakamakon gwajin da aka yi a ran 7 ga watan Faburairu a birnin Wuhan, Han ya yi amanna lokaci ya yi da zai yi ban kwana da mahaifinsa. Dukkanninsu sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Mahaifinsa, wanda ke cikin yanayi mai tsanani na cutar, an turashi zuwa asibitin musamman na Tongji. Yayin da aka tura Han zuwa asibitin wucin gadi, wanda ke da yawan gadaje kusan 1,500.

Asibitocin wucin gadi, wasu cibiyoyi ne aka mayar dasu asibitocin, sun taka rawar gani wajen dakile bazuwar kwayoyin cutar. Suna da yawan gadaje sama da 13,000 da aka kebe don duba mutanen da ake ganin suna da alamomin kamuwa da cutar don basu kulawar gaggawa.

Han, yana da alamu marasa tsanani, ana kula dashi sosai a asibitin wucin gadi. Jami'an lafiya suna yin rawa tare da marasa lafiya domin rage musu damuwa. Bidiyonsu ya karade shafuka sada zumunta.

Ya zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu, kusan mutane 5,000 a Wuhan sun warke.

Asibitoci mafiya inganci a Wuhan an kebe su domin kula da marasa lafiya kamar mahaifin Han. Ya zuwa 20 ga watan Fabrairu, akwai irin wadannan asibitoci kimanin 48, kuma da wuya su iya daukar marasa lafiya 10,000 dake cikin yanayi mai tsanani.

Baki daya jami'an kiwon lafiya 42,000 aka tura lardin Hubei don yaki da annobar. Wasu kwararru da tawagar jami'an lafiya daga wajen lardin Hubei sun tafiyar da sassan kula da masu fama da cuta mai tsanani wato ICU. An samar da na'urorin samar da iska ECMOs wato huhun roba da aka kaisu daga sassan kasar Sin zuwa lardin.

Likitoci sun sadaukar da rayuwarsu don ceto marasa lafiyar dake cikin hali mai tsanani. Dole ne a gudanar da aikin ceton cikin sauri, a cewar likitocin sashen ICU na asibitin Tongji inda ake kula da lafiyar mahaifin Han, sabida yanayin lafiyar majinyatan dake sashen tana neman tabarbarewa. Dokar asibitin shine: bibiyar yanayin lafiyar majinyatan dake sashen a duk tsawon sa'o'i 24.

Ana cigaba da ayyukan duba marasa lafiyar, da suka hada da taimakawa hanyoyin numfashinsu, da wasu dabarun zamani na ceto majinyata. Magungunan gargajiyar kasar Sin sun taimaka wajen warkar da marasa lafiya masu dunbun yawa da kuma takaita yawan lokutan da ake shafewa wajen aikin kula da marasa lafiya.

Ya zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu, sama da marasa lafiya 10,000 ne suka warke a Wuhan. Bayan kwanaki uku kuma, yawan mutanen ya karu zuwa 15,000. Bayan kwanaki biyar, sun karu zuwa 25,000. Daga cikin mutanen da suka warke har da wani dattijo dan kimanin shekaru 100 da matashi dan shekaru 17 da haihuwa.

Han da mahaifinsa a yanzu an killacesu bayan sun warke daga cutar. Ana jiran sake haduwarsu da juna.

To sai dai kuma, wasu likitocin basu tsira ba daga annobar. Sun kasance a matsayin jarumai na hakika a yaki da cutar COVID-19. A lardin Hubei kadai, sama da jami'an lafiya 3,000 ne suka kamu da cutar. Daga cikinsu 31 sun mutu, wanda ya hada har da shugaban asibiti.

Dr. Bruce Aylward, shugaban tawagar jami'an lafiya na hadin gwiwar Sin da hukumar WHO a yaki da cutar COVID-19 ya ce, idan ana son tabbatar da samun nasarar yaki da annobar da ta barke a sauran wurare kamar yadda Sin ta gudanar ana bukatar daukar matakan gaggawa, da samar da kudaden gudanarwa, da kyakkyawan tunani da kwarin gwiwar shugabanni.

Yayin da annobar ke cigaba da bazuwa a fadin duniya, ta hanyar yin hadin gwiwa da juna ne kadai za'a iya cimma nasarar yakar babbar abokiyar gabar wato cutar COVID-19. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China