Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yancin Magana Ba Zai Zama Hujjar Jaridar "The Wall Street" Ta Aikata Mugun Laifi Ba
2020-03-15 20:14:11        cri

Kwanan baya, wani matashi ya zargi wani dan asalin Asiya mai shekaru 59 a yankin Upper east Manhattan na birnin New York, inda ya kori wannan dan asalin Asiya da ya koma gidansa, tare da kiransa "cutar COVID-19".

Cikin dogon lokacin da ya gabata, ana gamuwa da matsalar nuna wariyar launin fata a kasar Amurka, har ta zama hujja ta masu ra'ayin nuna wariyar launin fata, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19. Kamar wani sharhin da jaridar "The Wall Street" ta fidda mai taken "kasar Sin ita ce mai rashin lafiya a nahiyar Asiya", ta hura wutar wariyar launin fata, lamarin da ya sa, gamayyar kasa da kasa suka yi Allah wadai da sharhin.

Ana ganin cewa, wasu 'yan kasar Amurka ba su son nuna amincewarsu kan ra'ayin wariyar launin fata a fili, shi ya sa, 'yancin Magana ya kasance hujjar masu wariyar launin fata, wannan shi ne dalilin da ya sa, a lokacin nan na barkewar cutar numfashi ta COVID-19, wasu 'yan Amurka sun ci gaba da tada hankulan 'yan asalin Asiya dake kasar Amurka.

'Yancin magana da wasu 'yan siyasar kasar Amurka suke ikirari, cewar za a fadi kome da ake son fadi, lalle ba gaskiya ba ne. A hakika dai, dukkanin abubuwan da muka fada, in sun dace da moriyarsu, za su zama 'yancin magana, in ba su dace ba, wadancan 'yan siyasa za su nuna zargi.

Don haka, jaridar "The Wall Street" ta kan yi fuska biyu, ta kuma ki jin shawarar jama'a, ba ta son gyara kuskuranta.

Amma wariyar launin fata ya zama guba ga kowane zamantakewar al'umma, kuma kowace kafar watsa labarai dake son aikata laifi bisa hujjar 'yancin magana za ta hallaka kanta. Ya zuwa ranar 15 ga wata, sharhin mai cike da ra'ayin wariyar launin fata yana ci gaba da kasancewa a shafin intanet na jaridar "The Wall Street", wanda zai zama shaidar mugun laifin da wannan jarida mai shekaru sama da dari daya ta yi. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China