Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahukuntan Botswana sun yabawa kokarin kasar wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-15 16:36:02        cri
Jami'an gwamnatin kasar Botswana sun yabawa kasar Sin bisa ci gaba da daukar matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a ciki da wajen kasar Sin, inda suka bayyana kwarin gwiwar ganin bayan annobar cutar a cikin kankanin lokaci.

Shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi ya yabawa matakan ayyukan kandagarki da magance cutar wadanda kasar Sin ke ci gaba da gudanarwa da nufin kawar da cutar a duniya baki daya.

A jawabin da ya gabatar ga jami'an lafiya a Francistown, birni na biyu mafi girma a kasar Botswana, Masisi ya ce, annobar cutar tana ci gaba da raguwa matuka a kasar Sin sakamakon kwararan matakan da kasar ke dauka na dakile cutar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China