Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace kasa da kasa su hada kai domin dakile cutar COVID-19 cikin hanzari
2020-03-14 20:28:11        cri
Yanzu gaba daya kasashe da yankunan fadin duniya da yawansu ya kai 123 sun gabatar da rahoton samun mutane sama da dubu 132 wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, a ciki, mutanen da suka rasu sun zarta 5000, lamarin da ya sa aka shiga lokaci mafi muhimmanci na dakile annobar. A kusan sa'i guda, gwamnatocin kasashen Turai sun kara tsattauran matakan shawo kan annobar daga dukkan fannoni. Amurka ma ta sanar da cewa, ta shiga yanayi mai tsanani. Firayin ministan Jamus Angela Merkel, ta jaddada cewa, dole ne a dauki matakai cikin gaggawa domin hana yaduwar annobar.

A karkashin irin wannan yanayi, kafofin watsa labaran kasashen yamma wadanda suka taba sukar kokarin da kasar Sin take na yakar annobar su ma sun amince cewa, kasashen duniya sun bata lokaci mai dajara da kasar Sin ta samar musu, kuma idan ba su himmantu ba, tattalin arzikin duniya zai dagule sanadin tasirin annobar.

Har kullum kasar Sin tana daukar hakikanin matakai domin yaki da annobar tare da sauran kasashe, alal misali ta kafa kungiyar kwararru cikin hadin gwiwa da kasashen Turai, ta kuma samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya cikin gaggawa ga kasashe da dama da suke bukata, kana ta tura kwararrun da abin ya shafa zuwa kasashen Iran da Iraki da Italiya da sauransu domin yaki da annobar tare, ban da haka, gwamnatin kasar Sin ta samar da tallafin kudi dalar Amurka miliyan 20 ga hukumar lafiya ta duniya domin taimakawa kasashe masu tasowa a bangaren. Duk wadannan matakan da kasar Sin ta dauka sun samu jinjina daga MDD da hukumar lafiya ta WHO. A jiya, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, alkaluma da bayanan da kasar Sin ta samar wa kasarsa za su taimaka mata matuka, shi ma ya amince cewa, kasar Sin ta samu sakamako a bayyane kan aikin dakile annobar.

Annoba tana shafar daukacin kasashen duniya, idan ana son cimma burin ganin bayanta, dole ne kasashen duniya su hada kai cikin hanzari.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China