Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Batun hakkin dan Adam na yankin Xinjiang karyar siyasa ce
2020-03-13 20:05:46        cri

Tun daga yau ranar 13 ga wata, aka dakatar da taron majalisar kiyaye hakkin dan Adam na MDD karo na 43, wanda ake gudanarwa a birnin Geneva a sanadiyar tasirin bazuwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma wasu kasashe, ba su daina zargin kasar Sin game da batun yankin Xinjiang na kasar ta Sin ba.

Kwanan baya, Amurka ta fitar da rahoton kiyaye hakkin dan Adam a wasu kasashe na shekarar 2019, inda ta sake sukar yanayin kiyaye hakkin dan Adam da kasar Sin ke ciki, da manufar da kasar take aiwatarwa a yankin Xinjiang, har ma ta yi zargin cewa, an tsare 'yan kabilar Uygur a wasu sansanin musamman. To sai dai kuma wadannan jita-jitar da ake bazawa, ba ta da tushe ko kadan, ana ma dai iya cewa karya ce kawai aka tsara saboda dalilan siyasa, kuma yunkurinsu shi ne kawo illa ga kokarin da kasar Sin take yi, domin yaki da ta'addanci a yankin Xinjiang, tare kuma da hana ci gaban kasar.

Sansanin musamman da wasu Amurkawa suka bayyana an tsare 'yan kabilar Uygur, cibiya ce ta horas da sana'o'i da aka kafa domin sauya tunanin masu tsattsauren ra'ayi, tare kuma da kyautata rayuwarsu.

A karshen shekarar bara, wani jami'in yankin ya taba bayyana cewa, daukacin daliban da suka shiga kwas din horaswar sana'o'i sun riga sun kammala karatunsu a cibiyar, haka kuma sun riga sun samu aikin yi a karkashin taimakon gwamnatin yankin. A cikin shekaru uku da suka gabata, babu aikin ta'addanci ko daya da ya faru a yankin Xinjiang, dalilin da ya sa haka shi ne, an aiwatar da matakai a jere da gwamnatin kasar Sin ta dauka a yankin, ciki har da kafa cibiyar horaswar sana'o'in.

A watan Yulin shekarar 2019, kasashe 51 wadanda ke kunshe da kasashe mambobin kungiyar hada kan musulmai 28, sun aike da sako ga shugaban majalisar kiyaye hakkin dan Adam ta MDD, da manyan jami'an da abin ya shafa, inda suka jinjinawa manufar yaki da ta'addanci da kasar Sin ke aiwatarwa a yankin Xinjiang, da kuma kulawar da gwamnatin kasar take nunawa musulmai.

Game da zargin da ake yi cewa, an hana a gudanar da harkokin addini a yankin Xinjiang, shi ma ba shi da tushe, domin kuwa a yanzu haka, adadin masallatai da aka gina a fadin kasar Sin sun kai fiye da 35000, adadin ya fi na kasashen Faransa, da Amurka, da Birtaniya yawa, duba da cewa adadin masallatan kasar Faransa ba su wuce 2300 ba, adadin a Amurka bai wuce 2,106 ba, kuma na Birtaniya bai haura 1600. A hakika a yankin Xinjiang, kusan musulmai 530 suna da mallaci masallaci guda daya.

Dalilai na zahiri sun shaida cewa, batun yankin Xinjiang na kasar Sin bai shafi hakkin dan Adam, ko addini ko kabila ba, kawai dai batu ne da ke shafar yaki da ta'addanci, da kuma dakile haifar da baraka ga kasa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China