Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe asitibocin wucin gadi dake birnin Wuhan
2020-03-15 20:21:30        cri

A ranar 10 ga wata, an rufe dukkanin asibitocin wucin gadi 16 dake birnin Wuhan na lardin Hubei. A ranar 5 ga watan Fabrairu ne, aka fara kwantar da wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a asibitocin wucin gadin, bayan kwanaki 35, aka salami dukkanin marasa lafiyan dake jinya a asibitoci, bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar. A karshe za a yi galaba a kan wannan annoba, kuma ba za a kara ganin wadannan asibitocin ba. A ranar 9 ga wata ne, ma'aikatan asibitin suka sanar da kawo karshensu a wajen, inda suka yi bankwana da maras lafiya. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China