Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya kira taron kungiyar jagorancin aikin dakile cutar COVID-19
2020-03-12 20:58:09        cri
A yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya kira taron kungiyar jagorancin aikin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 na kwamitin tsakiya na JKS, inda ya bukaci da a tabbatar da aikin dakile annobar bisa sauyin yanayin da annobar ke ciki, tare kuma da hana shigowar masu dauke da cutar daga ketare.

Yayin taron, an jaddada cewa, birnim Wuhan da lardin Hubei, za su ci gaba da kara karfafa aikin kula da masu dauke da cutar, wadanda ke cikin yanayi mai tsanani, da aikin hana bazuwar cutar a cikin unguwanni, tare kuma da ba da tabbaci ga zaman rayuwar al'ummun lardin. Kana hukumomin da abin ya shafa, za su kara daukar matakai domin hana shigowar masu dauke da cutar daga ketare, ko fitar masu dauke da ita zuwa ketare.

Ban da haka kuma, kasar Sin za ta samar da tallafi ga kasashe, da kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa, kana kamfanonin kasar su ma za su samar da karin kayayyakin kandagarkin annobar, domin biyan bukatu a cikin gida, da kuma sayar da su zuwa ketare bisa ka'idar kasuwa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China