Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar gudanarwar Sin ta fitar da sabbin manufofin sa kaimi kan cinikin waje
2020-03-11 21:07:06        cri
Jiya 10 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya kira taron majalisar gudanarwar kasar Sin, inda ya sanar da sabbin manufofin sa kaimi kan cinikayyar waje, da kara samun jarin waje, a yanayin da ake ciki na kokarin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, kana ya tsara mnufofin kyautata jerin ayyukan masana'antu, tare kuma da samar tallafi ga kamfanoni domin dawowa bakin aiki. Ban da haka, ya bukaci bankunan kasar da su samar da karin rancen kudi da kudin rangwame, ta yadda za a tabbatar da aikin samar da isassun kayayyakin da ake bukata, yayin da ake kokarin dakile annobar, tare kuma da taimakawa kamfanonin kasar domin su kubutar da kansu daga mawuyancin hali a sanadiyar barkewar annobar.

Yayin taron, an jaddada cewa, idan tana son ingiza ci gaban tattalin arziki, dole ne kasar Sin ta nace kan manufar bude kofa ga ketare, tare kuma da fitar da wasu sabbin manufofi na sa kaimi kan cinikayyar waje, alal misali mayar da haraji ga wasu kayayyakin da aka fitar zuwa ketare, da samar da karin rancen kudi kan cinikayyar waje, da rage kayyadewa 'yan kasuwan ketare dama ta yadda za su kara zuba jari a kasar, da tabbatar da daidaito tsakanin kamfanonin kasar da na katare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China