Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Sin na fatan kasashe biyar masu mallakar makaman nukiliya za su hada kai domin kiyaye tsarin kwance damara
2020-03-11 20:43:21        cri
Kasashe biyar masu mallakar makaman nukiliya wato Sin, da Faransa, da Rasha, da Birtaniya, da Amurka, sun jaddada cewa za su cika alkawari kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. Kan wannan batu, a yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kasashen biyar, za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin kiyaye tsarin kwance damara a fadin duniya, tare kuma da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen dokokin kasa da kasa.

A jiya ministocin harkokin wajen kasashen biyar, sun fitar da wata hadaddiyar sanarwar kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, inda suka nuna cewa, za su nuna goyon baya ga yarjejeniyar a bangaren siyasa, amma a sa'i daya, sun nuna damuwa kan makomar yarjejeniyar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China